GidaAzkarDaga cikin falalar tasbihi da tahmidizikiri 5

Daga cikin falalar tasbihi da tahmidi — zikiri 5

فضل التسبيح و التحميد، و التهليل، و التكبير · Hisnul Muslim · 5 / 12

Karanta · SauraraFayilar PDF

وَقَالَ صلى الله عليه وسلم: ((أَيَعْجِزُ أَحَدُكُم أَنْ يَكْسِبَ كُلَّ يَوْمٍ أَلْفَ حَسَنَةٍ)) فَسَأَلَهُ سَائِلٌ مِنْ جُلَسَائِهِ كَيْفَ يَكْسِبُ أَحَدُنَا أَلْفَ حَسَنَةٍ؟ قَالَ: ((يُسَبِّحُ مِائَةَ تَسْبِيحَةٍ، فَيُكتَبُ لَهُ أَلْفُ حَسَنَةٍ أَوْ يُحَطُّ عَنْهُ أَلْفُ خَطِيئَةٍ)).

Ma’ana: Manzon Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi ya ce; “A yanzu dayan ku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowacce rana?, Sai wani mutum cikin wadanda suke zaune tare da shi ya ce; Ta yaya dayan mu zai aikata ayyuka dubu?. Sai Ma’aikin Allah  ya ce: Ya yi Tasbihi dari, (yace: سُبْحَانَ اَللهِ) Tsarki ya tabbata ga Allah! Sau dari, sai a rubuta masa kyawawan ayyuka dubu ko a kankare masa zanubai dubu.

Saurara · Muryar Hamad al-Duraiham

Azkar · 15 harsuna