((اللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ، أَنْتَ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ، وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ قَيِّمُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ، [وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ رَبُّ السَّمَواتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ] [وَلَكَ الْحَمْدُ لَكَ مُلْكُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيهِنَّ] [وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ مَلِكُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ] [وَلَكَ الْحَمْدُ] [أَنْتَ الْحَقُّ، وَوَعْدُكَ الْحَقُّ، وَقَوْلُكَ الْحَقُّ، وَلِقاؤُكَ الْحَقُّ، وَالْجَنَّةُ حَقٌّ، وَالنَّارُ حَقٌّ، وَالنَّبِيُّونَ حَقٌّ، وَمحَمَّدٌ صلى الله عليه وسلم حَقٌّ، وَالسّاعَةُ حَقٌّ] [اللَّهُمَّ لَكَ أَسْلَمتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خاصَمْتُ، وَإِلَيْكَ حاكَمْتُ. فَاغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ، وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ، وَمَا أَعْلَنْتُ] [وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي] [أَنْتَ المُقَدِّمُ، وَأَنْتَ المُؤَخِّرُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ] [أَنْتَ إِلَهِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ] [وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ])).
Ya ubangiji dukkan yabo ya tabbata a gareka, kaine hasken sammai da kassai da abinda ke cikin su, dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine mai tsayar da sammai da kassai da abinda ke cikin su, [dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine ubangijin sammai da kassai da abinda ke cikin su] [dukkan yabo ya tabbata a gareka mulkin sammai da kassai da abinda ke cikin su naka ne] [ dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine mamallakin sammai da kassai ] [ dukkan yabo ya tabbata a gareka kaine gaskiya, alkawarinka shi ne gaskiya, fadar ka ita ce ta gaskiya, haduwa da kai tabbas ne, aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce, annabawan ka gaskiya ne, muhammadu mai tsira da aminci gaskiya ne, tashin alkiyama gaskiya ne, ] [ yaa Allah gareka na mika wuya, kuma da kai kadai na dogara, kuma da kai kadai nayi imani, kuma zuwa gareka kadai na ke komawa, kuma saboda kai kadai nake jayayya, kuma gareka kadai na kai hukunci. Don haka ka gafarta mini abinda ya wuce, da abinda zai zo nan gaba, da abinda na boye, da abinda na bayyana, da abinda kai ka fini sanin abinda na aikata, kaine mai gabatarwa, kuma kaine mai jinkirtarwa, babu abin bautawa bisa can-canta sai kai kadai, kaine abin bauta ta babu abin bauta bisa can-canta sai kai. Babu dabara babu karfi sai ga Allah.
Saurara · Muryar Hamad al-Duraiham