قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: ((إِذَا عَادَ الرَّجُلُ أَخَاهُ الْمُسْلِمَ مَشَى فِي خِرَافَةِ الْجَنَّةِ حَتَّى يَجْلِسَ، فَإِذَا جَلَسَ غَمَرَتْهُ الرَّحْمَةُ، فَإِنْ كَانَ غُدْوَةً صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ أَلْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُمْسِيَ، وَإِنْ كَانَ مَسَاءً صَلَّى عَلَيْهِ سَبْعُونَ أَلْفَ مَلَكٍ حَتَّى يُصْبِحَ)).
Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce: Idan mutum ya gaida dan’uwansa musulmi da ba shi da lafiya, to ya tafi ne akan hanyar aljanna har ya zauna, idan ya zauna kuma rahama ta lullube shi. Idan da safe ne mala’iku dubu saba’in ne za su yi masa salati har yamma ta yi. Idan kuwa da yamma ne to mala’iku dubu saba’in za su yi masa salati har gari yaw aye
Saurara · Muryar Hamad al-Duraiham